[Skip to Content]

IBA Montage

Muna gayyatar ƙungiyar ka ta aiko zabuka na Gasar Stevie® ga Manyan Masu Dauka Mutane Aiki (Stevie® Awards for Great Employers) na shekarar 2024 (a cikin shekara ta 9th), gasar girmamawa ajin farko a duniya ta nasarori a albarkatun mutane, tawaga, kwararru, da sabbin kayayyaki da sabis, da masu ba da kaya, waɗanda ke taimakawa ƙirƙirar da fitar da manyan wurare don aiki masu kyau.

Idan kuna son a aiko muku takardun shiga gasar, mai dauke da kaidojin yadda za a shiryawa shiga gasar da kuma mika cikakkun takardun shiga gasar, sai ku shighar da adireshin imel dinku a nan, mu kuma za mu aiko muku su ta imel.  Muna da tsarin tsare-sirri mai karfi kuma ba za mu bawa kowa adireshin imel dinku ba saboda kowanne dalili.

Wannan shafin shi ne kadai za ku gani a wannan shafin na intanet a cikin wannan harshen.  Dukkan sauran shafukan suna kunshe ne da bayanai cikin turancin Ingilishi, kamar su ma takardun shiga gasar.  Hakan ta faru ne saboda mun bukaci da a gabatar da bukatar shiga gasar cikin turancin Ingilishi, domin kwararru kan harkokin kasuwanci a duk fadin duniya su taka rawa wajen tantance wadanda suka shiga gasar.  Wadanan sune takaitaccen bayanai game da lambobin yabon, bukatun gabatarwa, da kuma amfanin shiga. Idan kun yanke shawara cewa ƙungiyar ku za ta aiko zabukanta domin lambobin yabo, ku tuna cewa dole ne ku shirya zabukanku cikin harshen Ingilishi.

Game da Stevie® Awards for Great Employers

Stevie Awards for Great Employers shi kadai ne shirin dake bada lambobin yabo na fid da masu aiki game da albarkatun mutane da kwararru na duniya baki daya.  Kungiyar shirya gasannin ta Stevie Awards, wacce take bada lambobin yabon, mazauninta na Amurka.  Sune masu shirya gasannin Cin Lambobin Yabo ta Stevie Awards daban daban guda takwas wanda za ku iya samun bayani game da su a www.StevieAwards.com.  Gasar cin lambar yabo ta Stevie Awards ta zama daya daga cikin lambobin yabo na duniya da ake girmamawa.

A shekara 2023, an bayar da lambar girmamawa ta Gasar Stevie ga Manyan Masu Dauka Mutane Aiki (Stevie Awards for Great Employers) ga kungiyoyi da daidaikun mutane daga kasashe 28. Latsa nan don ganin wadanda suka yi nasara a zangon 2023.

Rukuni-Rukuni

Akwai ire-ire guda shida na rukunonin lambobin yabo da za a iya zaba a Stevie Awards for Great Employers.  Idan kuka zabi shiga gasar, za ku zabi rukunin da ya dace da nasarorinda kungiyar ku ta samu kuma take son a karrama ta a kai, ku kuma shirya takardun shiga gasar bisa kaidojin da aka gindaya.  Rukuni-rukunin gasar da ake da su, sun hadar da :

Jeri da bayanan rukunonin ya na cikin takardun shiga gasar. 

A dukkan bangarorin zaku sami dama ku bayar da rubutattun amsoshi ma tambayoyin, ko bidiyo mai tsahon mintina biyar (5) waɗanda ke amsa tambayoyin.

Tuntuba

Lambar Yabo ta Stevie Awards na da wakilai a kasashe da dama. Wadannan wakilai za su raba bayanai su kuma taimakawa kamfanoni a kasashensu wajen shiga gasar cin lambar yabon.

Domin tantancewa ko akwai wakili a kasar ka, latsa nan.

Za ku kuma iya tuntubar masu shiryawa a wannan adireshi mai zuwa:

The Stevie Awards
10560 Main Street, Suite 519
Fairfax, Virginia 22030, USA
Lambar Waya: +1 703-547-8389
Fax: +1 703-991-2397
Imel: help@stevieawards.com

Share